Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin ƙwararru mai mambobi 20 domin nazari kan yadda za’a aiwatar da sabon tsarin albashi da aka amince da shi ga malaman makarantun gaba da sakandare mallakin ta.
Shugabar ma’aikatan gwamnatin Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota ce ta ƙaddamar da kwamitin, bayan amincewar gwamna Abba, biyo bayan buƙatun da malaman suka gabatar kan aiwatar da sabon tsarin albashin da gwamnatin tarayya ta amince da shi.
Mai mota ta ce an zaɓi mambobin kwamitin ne bisa ƙwarewa da gogewa, tare da umartar su da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya da kishin ƙasa, domin samarwa gwamnati rahoton da zai taimaka wajen yanke hukunci bisa ƙa’idojin da suka dace.
Daga cikin ayyukan kwamitin akwai tattarawa tare da nazarin buƙatu da takardun da cibiyoyin ilimi suka gabatar, da kwatanta tsarin albashin da ake bi a halin yanzu da sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta amince da shi, tare da tantance nauyin kuɗin da aiwatar da tsarin zai ɗorawa kasafin kuɗin jihar.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa kwamishinan Ilimin Kano, Dr Ali Haruna Makoda ne zai jagoranci kwamitin, yayin da aka baiwa mambobinsa makonni uku domin kammala aikinsu tare da miƙa cikakken rahoto ga ofishin Shugabar Ma’aikatar, wanda daga bisani za’a gabatarwa da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
