Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce harshen Hausa da al’adunsa na ɗaya daga cikin ginshiƙan asalin nahiyar Afirka, wanda yake samar da haɗin kai da ci gaba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin sakon taya al’ummar Hausawa da ke Najeriya da sauran sassan duniya murnar ranar Hausa ta duniya ta shekarar 2026.
Gwamnan ya ce taken bikin na bana, wato al’adunmu, makomarmu, na tunatar da al’umma muhimmancin kare harshe, al’adu, tarihi da kyawawan ɗabi’u domin amfanin al’ummomi masu zuwa.
Gwamnan ya ce ranar Hausa ta duniya, wadda aka ƙaddamar a shekarar 2015, ta bunƙasa zuwa matakin duniya, la’akari da yadda harshen yake ci gaba da yaɗuwa wajen nunawa da kare ɗimbin al’adun Hausawa, tare da yabawa da zaɓen birnin Daura a matsayin cibiyar bikin na bana.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na buƙatar Hausawa, musamman matasa, su yi alfahari da harshensu da al’adunsu, tare da amfani da fasahar zamani da ilimi wajen ƙara yaɗa harshen Hausa a duniya.
