Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da takwarorinsa na jihohin Yobe, Sokoto da Jigawa, sun jinjinawa Shugaban Majalisar Malamai ta ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, bisa ƙoƙarinsa na inganta haɗin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da sauran ’yan Najeriya.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne a wani taron ƙasa na yini guda da aka gudanar a birnin Jos, mai taken ƙarfafa shiga harkokin siyasa da tallafawa tabbatar da adalci domin samar da haɗin kai da ci gaban Najeriya.
A yayin taron, ƙungiyar JIBWIS ta yi kira ga mambobinta a faɗin Najeriya da su marawa Shugaba Tinubu da Kashim Shettima, baya tare da zaɓensu a babban zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban gudanarwa na ƙasa a ƙungiyar ta JIBWIS, Sheikh Abdulnasir Abdulmuhuyi, ya bayyana gamsuwar ƙungiyar da gwamnatin Tinubu da Shettima, yana mai cewa gwamnatin tarayya ta nuna ƙwazo da jajircewa wajen ci gaban Najeriya a cikin shekaru uku na farko na mulkinta.
Shi ma Shugaban Majalisar Malamai ta JIBWIS, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya buƙaci mambobin ƙungiyar a duk faɗin Najeriya su sabunta goyon bayansu ga Shugaba Tinubu da Kashim Shettima domin sake zaɓensu a shekarar 2027.
Da yake magana a madadin gwamnonin Kano, Sokoto, Jigawa da Yobe, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yabawa Sheikh Jingir bisa jajircewarsa wajen amfani da wa’azi domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da zaman lafiya tsakanin ’yan Najeriya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa, a nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ce ’yan Najeriya ba za su iya rasa gwamnatin Tinubu da Shettima a shekarar 2027 ba, yayin da shi ma ya yabawa Sheikh Jingir kan ƙoƙarinsa na tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya.
