Yayin da Najeriya ke shirin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027, hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ta yi gargadin cewa amfani da ƙirƙirarriyar basira (AI) wajen yaɗa bayanan ƙarya na iya zama babbar barazana ga sahihancin zaɓe.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya ce sahihancin zaɓe bai dogara da na’urorin fasaha kamar BVAS da takardun sakamako kaɗai ba.
Ya ce yadda ’yan Najeriya ke fahimtar bayanan da suka shafi zaɓe da kuma yadda suke tantance sahihancinsu na da matuƙar muhimmanci.
A wani jawabin da aka gabatar a madadinsa a taron shekara-shekara na 13 na Ƙungiyar Masana Sadarwa da Ƙwararrun Hulɗa da Jama’a ta Najeriya, shugaban INEC ya ce ya kamata a ƙara shigar da fasahar sadarwa cikin harkokin gudanar da zaɓe a ƙasar.
Ya kuma yi gargadin cewa ana iya amfani da AI wajen ƙirƙirar bayanan ƙarya, sauya hotuna da bidiyo, da kuma kwaikwayon muryoyin ’yan siyasa, lamarin da zai iya rikita masu kaɗa ƙuri’a gabanin zaɓen 2027.
Farfesa Amupitan ya jaddada buƙatar ƙara wayar da kan jama’a da kuma tabbatar da sahihancin bayanan da suka shafi zaɓe, domin dakile yaɗuwar bayanan ƙarya.
