Jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya bakwai sun gabatar da wani tsari na bai ɗaya ga Majalisar Ɗinkin Duniya, domin neman haɗin gwiwar ƙasashen duniya, kuɗaɗen raya ƙasa da zuba jari, da nufin buɗe damar tattalin arzikin yankin.
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma ce ta jagoranci shirin tare da haɗin gwiwar Shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na Raya Ƙasa (UNDP).
Ana sa ran za a gabatar da Tsarin Zaman Lafiya, Tsaro da Ci Gaban Arewa maso Yamma na shekarar 2026 zuwa 2030 a wani taro na musamman da za a gudanar a birnin New York a ranar Litinin, 21 ga Satumba, yayin taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81.
Taken taron shi ne: “Daga Rashin Kwanciyar Hankali zuwa Dama: Hanyoyin Samar da Zaman Lafiya, Juriya da Zuba Jari a Yankunan da ke Fuskantar Matsaloli.”
Jihohin Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara ne suka samar da tsarin, wanda ya mayar da hankali kan matsalolin tsaro, tattalin arziki da ci gaba da suka shafi yankin baki ɗaya.
Da take bayani a Abuja gabanin taron, wakiliyar UNDP a Najeriya, Elsie Attafuah, ta ce samar da zaman lafiya mai ɗorewa na buƙatar saka jari wajen magance matsalolin da ke haifar da rashin kwanciyar hankali.
Ta ce raunin hukumomin kakkabe talauci, ƙarancin abinci, sauyin yanayi da sauran rikice rikice na daga cikin abubuwan da ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro.
Ta ce tsarin ya kunshi yadda za a magance matsalar tsaro, samar da ayyukan jin ƙai, cigaban haɗin gwiwar jihohin yankin, tare da mayar da hankali kan sauya yanayin yankin wajen tabbatar da zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa.
