Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya tabbatar da shirin sayar da hannun jarin kamfanin takin zamani na Dangote, wato Dangote Fertiliser, zuwa kasuwar hannayen jari a shekarar 2028.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake yin barkwanci kan saƙonnin da sabbin masu hannun jarin matatar Dangote ke wallafawa a kafafen sada zumunta.
Dangote ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a taron Qatar Economic Forum ranar Lahadi, inda yake magana kan tsarin mallakar kamfanoninsa da kuma shirin jawo ƙarin masu zuba jari.
Ya ce kamfaninsa na neman ƙara yawan mutanen da za su zama abokan hulɗa ta hanyar mallakar hannun jari.
Da yake tsokaci kan barkwancin da ke yawo a kafafen sada zumunta, Dangote ya ce ya ga yadda wasu daga cikin waɗanda suka sayi hannun jarin matatar man fetur ɗinsa ke neman a kira taron kwamitin gudanarwa. Sabbin masu hannun jarin sun kasance suna wallafa hotuna da saƙonni cikin raha, suna nuna kansu a matsayin abokan mallakar matatar.
Rahotanni sun ce wannan barkwanci ya biyo bayan fara sayar da hannun jarin matatar man Dangote ga jama’a, da ya baiwa ƙananan masu zuba jari damar sayen hannun jari, lamarin da ya jawo hankalin jama’a da dama da kuma yawan saƙonni a kafafen sada zumunta.
Sanarwar shirin fitar da hannun jarin kamfanin takin Dangote a shekarar 2028 na nuna cewa rukunin kamfanin na shirin ƙara faɗaɗa damar mallakar hannun jari ga masu zuba jari.
Sai dai cikakkun bayanai kan ranar fara sayar da hannun jarin, farashinsa da tsarin IPO ɗin ba’a bayyana su ba tukuna.
