Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya yi maraba da matakin da malaman addinin Musulunci na jihohin Dandalin Masu Ilimin arewacin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar muslim Intellectual Forum suja ɗauka na goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran sa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa malaman bisa jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, tare da godiya ga shugabannin siyasa da malaman addinin.
Amincewar malaman dai na zuwa ne bayan wani taro da suka gudanar da gwamnonin jihohin Yobe, Sokoto, Jigawa, Kano, Kebbi, Katsina, inda Ministan gidaje da raya birane, Dr Muttaqa Rabe Darma, ya yi magana a madadin malaman, inda ya ce malaman sun gamsu da ci gaban da gwamnatin Tinubu ta samar wajen ginawa da gyaran hanyoyi da inganta tsaro da ilimi da harkokin lafiya da samar da ruwa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa malaman sun kuma yaba da gyaran hanyar Kano zuwa Kaduna, tare da ingantuwar tsaro a wasu sassan jihohin Kaduna da Katsina da Sokoto, sai dai sun buƙaci gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalolin tsaro da suka rage a jihohin Neja da Zamfara.
