Ma’aikata da iyayen ɗalibai sun rufe ƙofofin makarantun gwamnatin tarayya 120 da ake kira Unity Colleges a faɗin Najeriya, domin nuna adawa da shirin bai wa tsofaffin ɗaliban King’s College, Lagos, ragamar gudanar da makarantar.
An gudanar da zanga-zangar ne a lokacin da ya kamata makarantun su koma karatu, lamarin da ya kawo cikas ga fara sabon zangon karatu na shekarar 2026/2027.
Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, ASCSN, da ƙungiyar iyayen ɗalibai, PTA, sun shiga zanga-zangar a makarantu daban-daban. Wasu daga cikin ɗaliban da suka je makaranta domin komawa karatu ma an mayar da su gida.
A Abuja, ma’aikatan Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya sun tare ƙofar ma’aikatar, inda suka rike kwalaye masu ɗauke da saƙonnin adawa da shirin bai wa King’s College Old Boys’ Association, KCOBA, ragamar makarantar.
Babban sakataren ASCSN a King’s College, Ebenezer Oguntade, ya ce ma’aikatan na adawa da shirin ne saboda ba a shigar da muhimman masu ruwa da tsaki cikin tattaunawar ba.
Shi ma ma’ajin ƙungiyar iyayen ɗaliban King’s College, Emmanuel Abya, ya ce iyaye ba su amince da matakin ba, yana mai cewa ba a tuntube su yadda ya kamata ba.
Ya ce, “King’s College mataki ne na farko wajen karɓar sauran makarantun. Ya kamata gwamnatin tarayya ta ci gaba da tafiyar da makarantar da sauran makarantun, tare da samar musu da isassun kuɗaɗe.”
Rikicin ya samo asali ne daga umarnin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya na fara shirye-shiryen miƙa ragamar gudanar da makarantar King’s College ga KCOBA.
A wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 4 ga Satumba, 2026, ma’aikatar ta ce an kammala dukkan matakan da suka wajaba kafin sanya hannu kan yarjejeniyar bai wa ƙungiyar ragamar makarantar.
Ta ce za a kammala miƙa ragamar cikin watanni shida, sannan tallafin da makarantar ke samu daga asusun tarayya zai tsaya.
Sai dai gwamnatin tarayya ta musanta cewa an sayar da King’s College ko kuma an mayar da ita makaranta mai zaman kanta.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya ce yarjejeniyar ba ta sauya mallakar makarantar daga gwamnati zuwa KCOBA ba.
Ya ce, “Wannan yarjejeniya ba sayar da King’s College ba ce. Gwamnati ta ci gaba da riƙe haƙƙin mallakar makarantar, kuma za ta ci gaba da kula da yadda ake gudanar da ita.”
Gwamnatin ta ce KCOBA za ta samar da kuɗaɗen gyara da inganta gine-ginen makarantar, dakunan kwanan ɗalibai, dakunan gwaje-gwaje, ɗakunan karatu da sauran kayayyakin more rayuwa.
Ministan ya kuma ce yarjejeniyar ba ta tanadi ƙarin kuɗin makaranta kai tsaye ba, yayin da tsarin karɓar ɗalibai zai ci gaba da kasancewa bisa ƙa’idojin makarantun Unity Colleges.
Majiyar labari: The Sun.
