Gwamnatin Tarayya ta bayyana sabon shirin karbar bashin Naira biliyan 729 domin tallafa wa bangaren wutar lantarki, yayin da ake fuskantar gibin kudaden shiga da ake bukata wajen gudanar da harkokin bangaren.
Rahoton jaridar Guardian ya ce sabon bashin na zuwa ne a lokacin da bangaren wutar lantarki ke fuskantar matsalolin kudi da suka shafi kamfanonin samarwa da rarraba wutar lantarki.
Gwamnati na kokarin amfani da wasu hanyoyin samun kudade domin magance matsalolin da ke tattare da biyan bashin bangaren da kuma samar da jarin da ake bukata.
Masana sun dade suna cewa rashin isasshen jari da matsalolin tsarin biyan kudin wuta na daga cikin manyan dalilan da ke hana bangaren wutar lantarki samun kwanciyar hankali.
A gefe guda kuma, gwamnatin na neman kara yawan masu amfani da makamashin da ba nata ba, musamman hasken rana, domin rage matsin kan tsarin wutar lantarkin kasa.
Rahotanni sun ce Najeriya ta samu karin masu amfani da tsarin wutar lantarki na off-grid a cikin shekaru biyu da suka gabata, abin da ke nuna karuwar sha’awar amfani da hanyoyin samar da wuta daban da babban layin lantarki na kasa, national grid.
