Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya da hadin kan gwamnatin sa ga hukumar tara haraji ta Najeriya, NRS, domin karfafa hanyoyin samar da kudaden shiga da inganta tsarin karbar haraji a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar hukumar, wadda ta kai masa ziyara.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Dr Suleiman Wali Sani, ya ce tattaunawar da hukumar ke yi da masu biyan haraji a matakin kasa na da muhimmanci, duba da matsayin Kano na babbar cibiyar kasuwanci a arewacin Najeriya.
Gwamna Abba ya ce tattaunawar za ta taimaka wajen fahimtar kalubalen da masu biyan haraji, musamman ‘yan kasuwa da masu zuba jari ke fuskanta, tare da samar da manufofin da za su karfafa bin dokokin haraji da bunkasa kudaden shiga.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito shugaban tawagar, kuma daraktan sashin dake kula da harkokin gwamnati na hukumar, Wande Akinpelu, ya ce sun zo Kano ne domin tattaunawa da masu biyan haraji ta hanyar taron jin ra’ayin jama’a, da nufin gano matsalolinsu da samar da sauye-sauyen da za su saukaka biyan haraji.
