Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano SUBEB ta yi gargaɗi ga sakatarorin ilimi na ƙananan hukumomin kan gazawar kammala aikin ɗaukar bayanan makarantu na shekara-shekara, wato Annual School Census.
Shugaban Hukumar Malam Yusuf Kabir ya nuna rashin jin daɗinsa kan jinkirin, inda ya umarci sakatarorin ilimi da abin ya shafa da su gaggauta kammala aikin.
Wakiliyarmu Safina Abdullahi Hassan, ta zanta da daraktan wayar da kan jama’a na hukumar SUBEB Balarabe Danlami Jazuli, inda ya ce za’a dauki matakin kan duk wandada suka wuce ranar Talata basu kammala aikin ba.
A cewar Balarabe Danlami Jazuli, Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Takai, Kiru, Kumbotso, Dala, Nassarawa, Kura, Fagge da Tudun Wada.
