Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa da yawa daga cikin gwamnonin kasar nan sun fito ne daga cikin talakawa, amma a yanzu ana amfani da su wajen gallaza wa al’ummar da suka fito daga cikinta.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan halin da talakawan Najeriya ke ciki da kuma yadda ake tafiyar da mulki a wasu jihohin ƙasar.
Ya ce abin takaici ne yadda wasu shugabannin da suka taso daga cikin talakawa, kuma suka san irin ƙalubalen da talaka ke fuskanta, suke shiga tsarin da ke ƙara wa talakawa wahala.
A cewarsa, ya kamata shugabannin siyasa su yi amfani da matsayinsu wajen inganta rayuwar al’umma, samar da damarmaki da kuma rage wahalhalun da talakawa ke fuskanta, maimakon zama sanadin ƙarin matsin rayuwa.
Kwankwaso ya jaddada cewa kasar nan na buƙatar shugabanni masu tausayi da kishin al’umma, waɗanda za su sanya muradun talakawa a gaba wajen tsara manufofi da gudanar da mulki.
