Fadar Shugaban Najeriya ta bayyana kaɗuwa da rasuwar marigayi Sarkin Gumel Alhaji Ahmed Muhammad Sani, wanda Allah ya yiwa rasuwa a ranar Alhamis a ƙasar Masar kuma aka yi jana’izar sa a jiya juma’a a fadar sa dake Gumel yana shekera 84.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagoranci tawagar fadar ya zuwa sallar jana’izar marigayin wadda aka gudanar Masarautar Gumel dake jiharJigawa.
Shugaban wanda Mataimakin Sanata Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana marigayin a matsayin basarake mai daraja, wanda ya sadaukar da tsawon rayuwarsa wajen hidimtawa al’umma da samar da shugabanci nagari.
Daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar, akwai gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, wanda ya ce za’a ci gaba da tunawa da marigayin bisa kyawawan halayensa na shugabanci nagari, haƙuri, hikima da kuma juriya.
Wkilin mu na gidan gwamnati Kano Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa Gwamna Abba ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da sauran manyan masu riƙe da muƙaman siyasa.
