Gwamnatin Kano ta ce tana dab da fara tura ruwan sha na famfo sama da lita miliyan 40 ga al’ummar ƙwaryar birnin jihar, a yunƙurin ta na kawo karshen matsalar ƙarancin ruwa da ta daɗe tana addabar mazauna jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara domin duba yadda aikin gyaran rumbun ajiyar ruwa na Goron Dutse yake gudana.
Gwamna Yusuf ya ce aikin yiwa matsalar ruwan garanbawul, na daga cikin matakan da gwamnatin sa ke ɗauka don inganta samar da ruwan sha me tsafta domin rage wahalhalun da mazauna birnin Kano ke fuskanta a dalilin ƙarancin ruwan sha.
Da yake jawabi a wajen duba aikin, kwamishinan ma’aikatar ruwa, muhalli da sauyin yanayi Dr Dahiru Muhammad Hashim ya ce kamar yadda gwamnati tayi alkawari tun farko na kawo karshen matsalar tsaro ruwan sha a Kano a karshen December gwamnatin na gab da gama aikin kafin lokacin da tayi alƙawari.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamna Yusuf na jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar al’ummar Kano, musamman a fannin samar da ruwan sha mai tsafta da wadatar gaske.
