Gwamnatin Kano ta kaddamar da fara rarraba ruwan sha daga babban rumbun ajiyar ruwa na Goron Dutse, wanda ya kwashe sama da shekaru 30 baya aiki ya zuwa ƙwaryar birnin jihar.
Da yake jawabi a wajen, kwamishinan Muhalli, albarkatun ruwa da sauyin yanayi Dr Dahiru M Hashim ya ce dawo da rumbun Goron Dutse bakin aiki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Kano na farfaɗo da muhimman ababen more rayuwa da magance matsalar ƙarancin ruwan sha da ya daɗe yana addabar al’ummar birnin Kano.
Dr Dahiru ya ce rumbunan Goron Dutse guda uku na da ƙarfin adana kusan lita miliyan 40 na ruwa, inda mafi girman rumbun ke ɗaukar lita miliyan 22.5, yayin da sauran biyun ke ɗaukar lita miliyan 10 da miliyan 7.3.
Dr Dahiru ya ce yanzu ana ɗibar ruwa daga matatar Challawa zuwa rumbunan Goron Dutse me tsawon kilomita 15.6 domin rarrabawa ga al’ummomi a sassa daban-daban na birnin Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na cewa aikin gyaran ruwan ya lashe kuɗi fiye da naira biliyan 11, wanda kuma fara rarraba ruwan na nuna an samu gagarumin ci gaba a aikin kafin wa’adin da aka tsara na kammalawa a watan Disambar 2026.
