Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta kasa INEC, ta ce za a fara rabawa da kuma karɓar katunan zaɓe na dindindin, PVC, daga ranar 9 ga Oktoban 2026.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana hakan jiya Litinin a Kaduna, yayin taron tattaunawa na shiyyar Arewa maso Yamma da ma’aikatan hukumar, tare da tantance matakin shirin da aka ɗauka gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Farfesa Amupitan ya ce aikin rajistar masu kaɗa ƙuri’a na baya-bayan nan ya samar da sabbin rajista sama da miliyan 10.7.
Ya yi kira da a kawar da matsalolin da ke kawo cikas ga rabon katunan a matakin ƙananan hukumomi, domin kauce wa hana ’yan ƙasa da suka cancanta cin moriyar haƙƙinsu na zaɓe.
Haka kuma, ya ce INEC na inganta tsare-tsarenta na fasaha, ciki har da hanyoyin tantance masu kaɗa ƙuri’a da isar da sakamakon zaɓe, da kuma tsarin ƙirga sakamakon zaɓe.
