Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce gwamnatinsa za ta dawo da tallafin man fetur idan ta samu nasarar dakile cin hanci da rashawa.
Obi ya bayyana hakan ne a wani taron ganawa da jama’a da aka shirya domin yakin neman zabe jiya Litinin a Sakkwato.
Ya ce cin hanci da rashawa ne babban kalubalen da Najeriya ke fuskanta, yana mai cewa idan aka kawar da shi, za a samu damar dawo da tallafin mai.
Ya kuma ce ilimi zai kasance daya daga cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta fi ba wa muhimmanci, tare da tsaro, noma da sauran bangarorin tattalin arziki.
Obi ya kuma yi alkawarin hada manyan biranen jihohin kasar nan ta hanyar layin dogo domin bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki.
A nasa bangaren, abokin takararsa, Sanata Rabiu Kwankwaso, ya ce yankin Arewa maso Yamma na daga cikin wuraren da matsalar ’yan bindiga da satar mutane ta fi kamari, yana mai cewa za su mayar da hankali wajen magance matsalolin idan aka zabe su.
