Ana kuma sa ran Shugaban zai halarci bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Najeriya a Legas, kafin ya koma Abuja a karshen mako mai zuwa.
A ranar lahadi dai Majiyoyin fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa Tinubu zai shigo Najeriya ta Legas, inda ake sa ran Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, zai tarbe shi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed.
Shugaban ƙasar zai zauna a Legas har zuwa ranar yancin kai wato Alhamis, 1 ga Oktoba, inda zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya.
Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Tarayya ta bayyana cewa, matakin da Tinubu ya ɗauka na yin bikin ranar ‘yancin kai a Legas zai sa wannan ya zama shekara ta biyu a jere da Shugaban ke bikin ranar ‘yancin kan Najeriya a jihar.
Tun da farko dai Fadar shugaban kasa tace Tinubu zai dawo Najeriya bayan shafe makonni 3 yana hutu a Turai amma daga baya ta sanar da tsawita hutun shugaban.
Tsawaita hutun shugaban a kasashen Turai dai ya jawo cecekuce kan halascin wanda ke da ikon jan ragamar gwamnati musamman da shima mataimakin sa Kasshim Shettima ya bar Najeriya domin halartar taron majalisar dinkin Duniya a kasar Amurka.
