Iran ta musanta hannu a harin kunar bakin wake da aka kitsa kaiwa sansanin soji da ke kudancin Birtaniya.
A wata sanarwa da ofishin diplomasiyyar Iran a birnin Landan ya fitar, ya ce Tehran ta yi allawadai da duk wani abu da ya shafi labaran da ake yadawa kan wannan batu.
Rahotanni sun ce an kama mutum 5 ranar Lahadi, bayan gano wasu motocin daukar kaya 3 na tunkarar babbar kofar sansanin da sojin sama na Amurka ke amfani da shi wajen kai hari Iran.
Ƴansandan Birataniya sun ce dukkan mutanen 5 da ake tsare da su ‘yan Birtaniya ne, ana kuma zarginsu da laifukan ta’addanci da mallakar ababen fashewa.
Haka kuma Dukkansu mazauna birnin Landan ne kuma matasa dake tsakanin shekaru 20 da haihuwa.
