Wata cibiyar bincike da ke Jami’ar Chicago, Climate Impact Lab, ta Ƙiyasta cewa Ƙarin mutane dubu 66 da dari 800 na iya mutuwa a yankin Sahel tsakanin watan Satumba da Fabrairu, idan aka kwatanta da shekarun da yanayi yake bisa Ƙa’ida.
Najeriya ce ake hasashen za ta fi fuskantar mace-macen, da ƙarin mutane dubu 31 da dari 400, sai Sudan mai dubu 17 da dari 500, Nijar da dubu 10, sannan Chadi da dubu 8.
A duniya baki ɗaya, ana fargabar ƙarin mutane kusan dubu 239 za su mutu sakamakon matsanancin zafi a cikin watanni shida.
Wani masani a Jami’ar Chicago kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Climate Impact Lab, Michael Greenstone, ya ce adadin yana da matuƙar girma matuƙa.
El Niño wani yanayi ne da ke faruwa sakamakon ɗumamar ruwan tekun Pacific a yankin da ke kusa da Equator, wanda kan haifar da sauye-sauyen yanayi a sassa daban-daban na duniya.
Masu binciken sun ce El Niño na bana na iya zama mafi tsanani da aka taɓa gani a tarihi.
Masu binciken sun ce wasu daga cikin mafi yawan mace-macen na iya faruwa ne daga watan Disamba zuwa Fabrairu.
A Najeriya kadai, ana hasashen ƙarin mutane dubu 15 da dari 400 za su iya mutuwa sakamakon matsanancin zafi a wannan lokacin.
Masana sun ce matakan gaggawa kamar bayar da gargaɗin zafi, samar da wuraren sanyaya jiki, wuraren samun ruwa da kuma kare ma’aikatan da ke aiki a waje na iya taimakawa wajen rage mace-macen.
