Gwamnatin Tarayya ta nemi sabon tallafin kuɗi da ya kai dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya.
Rahoton Daily Trust ya ce ana shirin amfani da kuɗin wajen faɗaɗa shirye-shiryen tallafawa jama’a da inganta wasu fannoni na tattalin arziki.
Daga cikin abubuwan da shirin ya shafa akwai tallafin zamantakewa da inganta ilimin yara ƙanana.
Neman sabon bashin na zuwa ne yayin da gwamnatin Najeriya ke ƙoƙarin samun ƙarin kuɗaɗen aiwatar da shirye-shiryen raya ƙasa.
Gwamnatin kasar nan ta sha cewa irin waɗannan kuɗi za su taimaka wajen aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi tattalin arziki da jin daɗin jama’a.
