Rundunar sojin kasar nan ta ce dakarunta sun ceto mutane 41 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara, a yayin da suke kan hanyarsu daga Senegal zuwa Kano.
Rahoton ya ce matafiyan na cikin wata mota ta kasuwanci da ta samu matsala a hanya, lamarin da ya ba ’yan bindigar damar tare motar tare da yin awon gaba da mutanen.
Dakarun Operation Fansan Yamma ne suka gudanar da aikin ceton, bayan samun bayanan sirri kan inda aka yi garkuwar.
Rahotanni sun ce an samu nasarar kubutar da matafiyan ba tare da an rasa rayuka daga cikinsu ba, yayin da ake ci gaba da kokarin ganowa tare da kama ‘yan bindigar.
