Kamfanin Tianneng ya ƙaddamar da sabbin babura masu kafa biyu da masu kafa uku da ke amfani da wutar lantarki, a wani biki da aka gudanar a birnin Kano.
Taron ƙaddamar da kayayyakin ya samu halartar manyan ’yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci a jihar Kano, ciki har da Alhaji Sabiu Bako da Alhaji Tajjudin Aminu Dantata, tare da sauran fitattun ’yan kasuwa.
A yayin taron, kamfanin ya gabatar da wasu daga cikin sabbin fasahohinsa da suka shafi ababen hawa masu amfani da makamashin lantarki, waɗanda ake sa ran za su taimaka wajen samar da wasu hanyoyin sufuri na zamani a jihar Kano.
Haka kuma, Tianneng ya kulla yarjejeniyoyin haɗin gwiwa da wasu kamfanoni a Kano, da nufin faɗaɗa kasuwancinsa tare da ƙara samar da damar amfani da kayayyakin da kamfanin ke samarwa a Kano da sauran sassan Najeriya.
Taron ya kuma samar da wata dama ta haɗa kamfanin da ’yan kasuwa da masu zuba jari, inda aka tattauna hanyoyin haɗin gwiwa da kuma bunƙasa harkokin sufuri da ke amfani da makamashin lantarki.
Ana kallon ƙaddamar da waɗannan sabbin babura a matsayin wani mataki na ƙara faɗaɗa amfani da fasahar ababen hawa masu amfani da wutar lantarki a Kano da sauran sassan ƙasar.



