Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce lokaci ya yi da za’a ajiye son zuciya, munafurci da fuska biyu, tare da fito da matsayar kowa a fili wajen marawa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, baya domin neman tazarce a mulkin su.
Kwamared Waiya ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen taron saukar karatun Alƙur’ani mai girma, wanda ƙungiyar kansilolin da ke goyon bayan tazarcen Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaba Tinubu ta shirya.
A cewar Waiya, bai kamata mutum ya riƙa ɓoye matsayarsa ba, yana nuna goyon baya a ɓoye tare da yin abin da ya saɓa da hakan a fili, yana mai cewa lokaci ya yi da masu goyon bayan shugabannin biyu za su fito fili su bayyana matsayarsu.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Ƙungiyar kansilolin masu goyon bayan tazarcen Shugabannin biyu Kabiru Maresca Dala, ya ce sun shirya taron saukar ne domin neman zaman lafiya a Kano daga hare-haren ‘yan ta’adda da kuma neman yaddar Allah akan tazarcen na Shugaba Tinubu da Gwamna Abba.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Waiya na jaddada cewa haɗin kai da gaskiya su ne hanyoyin da za su taimaka wajen tabbatar da ci gaba da kuma samun damar sake baiwa Gwamna Abba da Shugaba Tinubu damar ci gaba da ayyukan da suka faro.
