Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce inda ana samun isasshiyar wayar da kai da sanar da al’umma irin ayyuka da nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu a arewacin Najeriya, da jama’ar yankin da kan su zasu yi masa yakin neman zaɓe da tabbatar da nasarar sa.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi bakuncin ƙungiyar Triple R, inda ya jaddada muhimmancin ƙara wayar da kan al’umma game da abubuwan da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa musamman a yankin Arewa.
Gwamna Yusuf ya ce idan ana samun ƙarin matasa da ƙungiyoyi irin su Triple R da ke wayar da kan jama’a tare da bayyana irin ayyukan da gwamnatin Tinubu ke kawowa Arewa, da mutane da dama sun fahimci abubuwan da gwamnatin ke yi.
A nasa jawabin shugaban ƙungiyar ta Triple R na ƙasa Dauda Kahutu Rarara, ya ce ba’a taɓa yin Gwamna mai haƙuri da juriya a Kano kamar gwamna Abba Kabir Yusuf ba, yana mai cewa waɗannan halaye sune suka bambanta shi da wadanda suka gabace shi wajen tafiyar da mulki.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gwamnan na yabawa ƙungiyar ta Triple R bisa ƙoƙarinta na wayar da kan al’umma da kuma nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC gabanin zaɓen shekarar 2027, tare da yin alkawarin tallafa mata wajen gudanar da ayyukanta.
