Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce halin da yake ciki da kuma shari’ar da yake fuskanta sun sa ya sake duba dangantakarsa da wasu daga cikin abokansa da abokan aikinsa.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce wasu daga cikin mutanen da ya taɓa mara wa baya sun yi shiru a lokacin da yake fuskantar matsaloli.
A cewarsa, abubuwan da ya fuskanta a cikin watannin baya sun koya masa darussa game da rayuwa, musamman yadda ake gane mutanen da ke da muhimmiyar alaƙa da mutum a lokacin ƙalubale.
Tsohon gwamnan na fuskantar shari’a da suka shafi zarge-zargen halasta kuɗaɗen haram, da kuma karkatar da kadarorin gwamnati. Hukumar ICPC ce ke tsare shi tun ranar 19 ga Fabrairu, bayan hukumar EFCC ta sake shi.
El-Rufai ya ce duk da cewa wasu daga cikin mutanen da ya taɓa mara wa baya ba su nuna goyon baya a lokacin da yake cikin wannan hali ba, ba ya nadamar taimaka musu a baya.
Ya ce ya mara musu baya ne bisa imaninsa, tarbiyyarsa da kuma abin da lamirinsa ya nuna masa a lokacin.
Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa ba ya neman ɗaukar fansa ko hukunta mutanen da suka zaɓi kada su mara masa baya a halin da yake ciki.
Ya ce zai bar hukunci na ƙarshe ga Allah, yayin da shi kuma zai ci gaba da mai da hankali kan kasancewa cikin kwanciyar hankali da lamirinsa da imaninsa.
El-Rufai ya ƙara da cewa lokaci ne zai nuna yadda mutane suka yi amfani da zaɓin da suka yi a lokacin da yake fuskantar wannan ƙalubale.
