Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin tarayya da ƙoƙarin ci gaba da tsare tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, har sai bayan babban zaɓen shekarar 2027 domin raunana haɗin kan jam’iyyun adawa.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan a shirin Politics Today na Channels TV, inda ya ce duk da cewa ana tuhumar El-Rufai da laifukan da doka ta tanadi yiwuwar bayar da beli a kansu, har yanzu ba a sake shi ba.
Abdullahi ya kuma ce bayanan da suka samu daga iyalan El-Rufai sun nuna cewa lafiyarsa na ci gaba da taɓarɓarewa, kuma likitoci sun ba da shawarar a ci gaba da kula da shi a asibiti.
Ya ƙara da cewa idan wani abu ya faru da tsohon gwamnan yayin da yake tsare, jam’iyyar ADC za ta ɗora alhakin hakan kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai a halin yanzu, ICPC da DSS na gurfanar da El-Rufai a gaban kotuna daban-daban bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa da kuma sauraron wayoyi ba bisa ka’ida ba. Haka kuma, kotuna sun sha yin watsi da buƙatunsa na beli.
