Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta sanar da cafke wani da ake zargi da damfarar wata mata mazauniyar Saudiyya kuɗi har ₦12,923,000 ta hanyar yaudara a shafin WhatsApp, yayin da ta ce ta samu wasu manyan nasarori a yaƙi da aikata laifuka a jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana cewa binciken da jami’an ’yan sanda suka gudanar ya kai ga cafke wanda ake zargin a Jihar Kaduna, bayan gano cewa ya yi amfani da asusun banki da lambar WhatsApp wajen aikata laifin.
Hakazalika, rundunar ta ce ta kama wata mata da ake zargi da yin almundahanar kuɗi har ₦10,500,000, sannan ta gano katunan ATM guda 36 a hannun wani da ake zargi da damfarar kwastomomi a bankuna.
A cewar rundunar, waɗannan nasarori sun samu ne sakamakon ingantaccen binciken sirri da kuma gaggawar da jami’anta ke yi wajen amsa kiran gaggawa.
Rundunar ta ƙara da cewa ana ci gaba da neman wasu da ake zargi da tserewa domin su fuskanci hukunci bisa doka.
