Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Manoma ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, Abdullahi Ali Mai Biredi, ya yi kira ga ƙananan manoma da su shiga ƙungiyoyin manoma domin samun damar cin gajiyar tallafi da shirye-shiryen da za su taimaka wajen bunƙasa harkokinsu.
Ya yi wannan kira ne bayan da Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa ƙananan manoma ne ke samar da kashi 85 cikin 100 na abincin da ake ci a Najeriya.
A cewar Abdullahi Ali Mai Biredi, duk da cewa ƙananan manoma ne ke samar da mafi yawan abincin da ake ci a ƙasar, su ne kuma ke fuskantar mafi yawan ƙalubale wajen bunƙasa ayyukan nomansu.
Ya ce shiga ƙungiyoyin manoma na bai wa manoma damar samun bayanai, horo da kuma tallafin da gwamnati da sauran hukumomi ke samarwa domin haɓaka noma.
Mai Biredi ya kuma yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafa wa ƙungiyoyin manoma da ƙananan manoma, tare da samar da kayan noma a farashi mai sauƙi da kuma a kan lokaci, domin ƙara yawan amfanin gona da bunƙasa harkar noma a Najeriya.
