Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, reshen Jami’ar Zamfara da ke Talata Mafara, ta bai wa Gwamnatin Jihar Zamfara wa’adin makonni biyu da ta fara aiwatar da sabon tsarin albashin malaman jami’ar, tare da biyan wasu basussukan da ake bin mambobinta.
ASUU ta ce idan gwamnatin jihar ta gaza cika buƙatunta cikin wa’adin da ta sanya, za ta ɗauki matakan da suka haɗa da rufe jami’ar da fara yajin aikin gargadi.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai rikon mukamin Sakatare Janar na reshen, Abdussamad Muhammad Usman, ya sanya wa hannu, bayan taron babban zartarwarta karo na biyu da aka gudanar a ranar 21 ga Satumba, 2026.
Shugaban reshen ASUU na jami’ar, Kwamared Anas Dogo, ya ce ƙungiyar ta yi ƙoƙarin warware matsalolin ta hanyar tattaunawa, amma hakan bai haifar da sakamakon da take tsammani ba.
A cewarsa, ASUU ta rubuta wasiƙun neman ganawa da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jihar, Shugaban Ma’aikatan Jihar da Kwamishinan Ilimi, domin tattauna batutuwan da suka shafi malaman jami’ar.
Dogo ya ce babban abin da ƙungiyar ke nema shi ne aiwatar da yarjejeniyar albashi da ASUU ta ƙasa ta cimma da Gwamnatin Tarayya a watan Disamba 2025, domin malaman Jami’ar Zamfara su samu irin tsarin da ake aiwatarwa ga malaman jami’o’in gwamnati a sauran sassan ƙasar.
Ya ƙara da cewa buƙatun ƙungiyar sun haɗa da biyan kuɗaɗen karin girma da sauran basussukan da suka taso tun bayan fara aiwatar da sabon tsarin.
ASUU ta ce za ta fi son a warware matsalar ta hanyar tattaunawa, amma ta gargadi gwamnatin jihar cewa rashin ɗaukar mataki cikin makonni biyun na iya haifar da katsewar ayyukan ilimi a jami’ar.
Rahotannin da suka fito daga Zamfara sun tabbatar da cewa batun aiwatar da yarjejeniyar ASUU ta 2025 ya jima yana cikin manyan ƙorafe-ƙorafen malaman jami’o’in jihar.
A halin yanzu, ASUU reshen Jami’ar Zamfara ta ce tana jiran matakin da gwamnatin jihar za ta ɗauka kafin wa’adin ya ƙare.
