Gwamnatin Kano ta amince da miƙa kwarya-kwaryar kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya kai naira tiriliyan 1 da biliyan 201, ga majalisar dokokin jihar domin yin nazari da amincewa da shi.
Kwamishinan yaɗa labarai Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar na 41.
Waiya ya ce najalisar zartarwar ta kuma amince da kashe naira biliyan 144 da miliyan 5 domin aiwatar da ayyukan more rayuwa da shirye-shirye daban-daban a faɗin jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan buƙatar gwamnati na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen raya jihar tare da samar da abubuwan more rayuwa ga al’umma.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa yanzu haka, majalisar dokokin ta Kano za ta yi nazari kan kwarya-kwaryar kasafin kuɗin kafin ta yanke shawarar amincewa da shi.
