Hukumar ula da gidajen ajiya da gyaran hali ta Najeriya ta ce ta shawo kan barkewar cutar kwalara da ta auku a gidan gyaran hali na Kurmawa, inda mutane biyu suka rasa rayukansu sakamakon cutar.
Hukumar ta ce an tabbatar da barkewar cutar ne ta hanyar gwaji da ƙwararrun tawagar likitocin hukumar suka gudanar.
A cewar kakakin hukumar, JN Osuji, lamarin ya fara bayyana ne ranar 17 ga Satumba, bayan da wani fursuna ya fara fama da amai da gudawa, inda aka garzaya da shi asibitin gidan gyaran halin domin ba shi kulawar gaggawa.
Hukumar ta ce ɗaya daga cikin wadanda suka mutu ya rasu ne a gidan gyaran halin, yayin da ɗayan ya rasu a Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa na Kano.
Sai dai hukumar ta ce tun bayan tabbatar da ɓullar cutar ba a sake samun wani mutuwa ba, bayan da aka ɗauki matakan gaggawa na dakile yaduwar cutar.
Hukumar ta ce tana yin haɗin gwiwa da gwamnatin Kano wajen ɗaukar ƙarin matakan kariya daga sake barkewar cutar, yayin da babban Kwanturolan Hukumar, Sylvester Ndidi Nwakuche, ya tura ƙwararrun likitoci daga hedikwatar hukumar domin ci gaba da sanya ido kan halin da ake ciki.
