Ƙungiyar Ma’aikatan Majalisun Dokoki ta Ƙasa (PASAN) ta bayyana Jihar Kano a matsayin jiha ta farko a Arewa maso Yamma da ta aiwatar da sabon tsarin albashin ma’aikatan majalisun dokoki na CONLESS gaba ɗaya.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran ƙungiyar, Tasi’u Jibo Dawanau, ya fitar, PASAN ta ce ta karrama shugabanni da mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano ta 10 bisa wannan nasara.
Mataimakin Shugaban PASAN na Arewa maso Yamma, Kwamared Yusuf Musa Dankado, ya bayyana cewa jihohi biyu ne kawai daga cikin bakwai na shiyyar suka aiwatar da tsarin gaba ɗaya.
Ya ce jihohin Jigawa da Zamfara sun aiwatar da wani ɓangare na tsarin, yayin da Kaduna, Katsina da Kebbi ke matakai daban-daban na aiwatarwa.
Sanarwar ta ce Dankado da Kwamared Nura Ginsau sun gabatar da lambobin yabo da takardun shaida ga shugabanni da mambobin majalisar.
Shugaban PASAN na Kano, Kwamared Murtala Badamasi Yusuf, ya kuma yaba wa ƴan majalisar bisa haɗin kan da suka bayar wajen aiwatar da sabon tsarin albashin.
