Kano: Kotu Ta Yanke Wa Matashin TikTok Hukuncin Shara Na Mako Biyu
Wata Kotun Majistare a Kano ta yanke wa matashin TikTok, Rabi’u Sani Zage, hukuncin yin shara na tsawon makonni biyu, bayan samunsa da laifin ɓata sunan ma’aikatan Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA).
Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima Wali, ta same shi da laifin wallafa bidiyoyin jami’an hukumar a TikTok tare da kalaman da ke ɓata musu suna.
A wata sanarwa da kakakin KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharada, ya fitar, hukumar ta ce kotun ta umarci matashin ya gudanar da aikin shara da tsaftace harabar hedikwatarta da ke Club Road a Kano na tsawon makonni biyu.
Kotun ta kuma umarce shi da ya rubuta takardar neman afuwa ga shugabancin KAROTA, tare da goge bidiyoyin da ya wallafa game da jami’an hukumar da kuma yin alƙawarin ba zai sake aikata irin laifin ba.
