Fadar shugaban Najeriya ta bayyana marigayi Hamza Darma a matsayin fitaccen ɗan siyasa, wanda gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Kano da Najeriya za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa.
Fadar ta bayyana hakan ne lokacin da wata babbar tawaga daga fadar shugaban ƙasar ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Hamza Usman Darma, fitaccen ɗan siyasa kuma dattijon ƙasa, wanda ya rasu a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Da yake isar da saƙon ta’aziyyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin tarayya ga iyalan marigayin da gwamnatin Kano, gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya ce, marigayin na daga cikin manyan waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu da abinda ya mallaka wajen gina kyakkyawar ƙasa me cike da al’umma ta gari.
Da yake jawabi a madadin iyalan marigayin, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa Shugaba Tinubu bisa babbar tawagar da ya turo Kano domin yin ta’aziyyar ɗaya daga cikin manyan iyayen ƙasa kuma masu kishi.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa tawagar ta ƙunshi mai baiwa shugaba Tinubu shawara na musamman, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da gwamnonin jihohin Yobe, Sokoto da Jigawa, tare da manyan ’yan siyasa, kwamishinoni da masu baiwa Gwamnan Kano shawara.
