Fiye da malaman addinin Musulunci, masu wa’azi da limamai 500 daga jihohin arewa 19 da birnin tarayya Abuja, sun bayyana goyon bayansu ga tazarcen Shugaba Tinubu a zaben shekarar 2027.
Malaman sun bayyana matsayinsu ne karkashin kungiyar Muslim Intellectuals Forum, a wani taro da aka gudanar a Jihar Jigawa, inda suka ce sun dauki wannan matsaya ne bisa la’akari da ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa da kuma irin tasirin da suke ganin ayyukan na yi wajen bunkasa yankin Arewacin Najeriya.
Da yake karanta kudurin taron a madadin malaman, ministan gidaje da raya birane, Dr Muttaka Rabe Darma, ya ce gwamnatin Shugaba Tinubu na samun ci gaba a bangarorin tsaro, samar da ababen more rayuwa da bunkasa tattalin arziki, musamman a wasu jihohin Arewa.
Shi ma shugaban kungiyar malaman, Sheikh Sale Abdullahi Pakistan, ya ce sun yi la’akari da manyan ayyukan da gwamnatin tarayya ke aiwatarwa a arewacin Najeriya, ciki har da aikin gyaran babbar hanyar Kano zuwa Kaduna, wanda ya bayyana ta a matsayin muhimmin aikin da zai taimaka wajen farfado da harkokin kasuwanci da tattalin arzikin yankin.
Malaman sun kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta ci gaba da kokarin inganta tsaro da samar da ayyukan raya kasa, inda suka ce arewa ta fara ganin wasu sauye-sauyen ci gaba a karkashin gwamnatin Shugaba Tinubu, duk da cewa akwai sauran aiki mai yawa, musamman wajen kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi wasu sassan yankin.
Wakilinmu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa daga cikin wadanda suka halarci taron akwai gwamnonin Jigawa, Kano, Yobe, Kaduna da Sokoto, da kuma wakilan gwamnonin Kebbi da Katsina, haka kuma taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, da mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabiru Masari.
