Hukumar Shari’a ta Kano ta gudanar da taron wayar da kan jama’a muhimmancin kalandar Musulunci, wadda gwamnatin jihar ta dauki nauyin samarwa domin amfanin al’ummar Musulmi.
Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishina na biyu a hukumar, Sheikh Ali DanAbba, ya bayyana muhimmancin kalandar da irin rawar da take takawa wajen tafiyar da harkokin ibada da rayuwar Musulmi.
Sheikh DanAbba ya ce kalandar tana da matukar amfani wajen tantance lokutan ibadu da suka hada da azumi, hajji da sauran muhimman al’amuran Musulunci.
A nasa bangaren, Malam Ibrahim Falaki, wanda ya gabatar da muƙala a wajen taron, ya yi bayani kan tarihin kalandar Musulunci da muhimmancinta ga Musulmi a fadin duniya.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito falaki na yin kira ga al’umma da su kara fahimtar amfani da kalandar Musulunci tare da kiyaye lokutan da aka tanada bisa tsarin addinin Musulunci.
