Gwamnatin Kano ta dakatar da tura ruwan famfo daga ma’ajiyar Goron Dutse zuwa birnin jihar na ɗan lokaci, bayan ƙarfin ruwan da aka saki ya haddasa fashewar wasu daga cikin bututun ruwa a sassa daban-daban na birnin Kano.
Kwamshinan Ma’aikatar Albarkatun ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi Dr Dahiru Muhammad Hashim ne ya bayyana hakan, inda ya ce matakin ya zama dole domin a baiwa hukumomi damar gyara bututun da suka fashe, bayan ruwan ya fara isa wasu sassan birnin Kano.
Kwamshinan ya ce da zarar an kammala gyare-gyaren, za’a ci gaba da tura ruwan kamar yadda aka tsara, hadi da jaddada cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da samar da ruwan sha ga al’ummar Kano.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Dr Hashim na buƙatar al’ummar Kano da su taimaka wajen sanar da hukumomi duk inda suka ga bututu ya fashe ko aka samu wata matsala da ta shafi rarraba ruwa, domin a dauki matakin gaggawa ta lambar waya 07078595955, ko adireshin imel kanoenvironment@gmail.com.
