Gwamnatin Kano ta ce manufofin tattalin arziki da inganta kasuwancin da ta ɓullo da su, sun buɗe sabbin damammaki ga ‘yan kasuwar jihar domin faɗaɗa harkokinsu zuwa kasuwannin ƙasashen duniya.
Babban Mai baiwa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf Shawara kan Harkokin Kasuwanni, Alhaji Abdurrahman Abubakar Gobirawa, shi ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai.
Gobirawa ya ce gwamnatin ta samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa ta hanyar inganta kasuwanni, sauƙaƙa gudanar da harkokin kasuwanci da bijiro da shirye-shiryen tallafa musu, musamman
sauƙaƙa hanyoyin samun takardun tafiye-tafiye da sauran buƙatun da suka shafi zirga-zirgar kasuwanci.
A cewarsa, gwamnatin Kano na ci gaba da gudanar da ayyukan gyare-gyare da inganta kasuwannin jihar musamman gina hanyoyi, ƙarfafa tsaro, samar da magudanan ruwa da samar da kayan more rayuwa domin bunƙasa harkokin kasuwanci.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Gobirawa na tabbatar da cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su ƙarfafa kasuwanci, zuba jari da bunƙasa tattalin arzikin Kano, tare da yin kira ga ‘yan kasuwa su ci gaba da amfani da damammakin da gwamnati ke samarwa.
