Shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da wani ƙaramin jirgin sojin Amurka wajen ficewa daga Turkiyya zuwa Birtaniya a asirce a watan Yulin da ya gabata, bayan rahotannin samun barazanar kai masa hari daga Iran.
Jaridar Washington Post da New York Times sun ruwaito cewa an aiwatar da wata dabarar tsaro ne bayan Trump ya halarci taron ƙungiyar NATO a Ankara.
Rahotanni sun ce duk da cewa an ga shugaban yana shiga tsohon jirgin shugaban Amurka, Air Force One, daga baya an mayar da shi cikin wani ƙaramin jirgin sojin Amurka kirar C-32A ta hanyar wata motar da ake amfani da ita wajen kai kayan abinci filin jirgin.
An kuma ce an yi amfani da tsohon jirgin Air Force One a matsayin dauke hankali, inda wasu ‘yan jarida da ma wasu ma’aikatan fadar White House suka yi zaton shugaban yana cikinsa.
Rahoton ya ce Trump ya isa sansanin sojin sama na RAF Mildenhall da ke Birtaniya kafin tsohon Air Force One, wanda ke ɗauke da ‘yan jarida da wasu ma’aikatan fadar White House.
Kafin tafiyar, Trump ya sanar cewa zai bar Turkiyya ne da tsohon Air Force One “saboda tarihi”, yayin da sabon Boeing 747-8 da Qatar ta bai wa Amurka kyauta zai tafi Birtaniya daban domin sojojin Amurka su samu damar duba jirgin.
Sai dai rahotannin sun ce a maimakon haka, an sauya Trump zuwa jirgin C-32A a asirce kafin jirgin Air Force One ya tashi.
An kuma umarci ‘yan jaridan da ke cikin jirgin bogin da su rufe tagogin jirgin a lokacin tafiyar, domin kada a gano cewa shugaban ba ya cikin jirgin.
Daga baya Trump ya bayyana a bainar jama’a a Birtaniya, inda aka gan shi yana shiga sabon jirgin da Qatar ta bai wa Amurka domin komawa Amurka.
Fadar White House ba ta tabbatar da cikakkun bayanan wannan shirin ba, amma Daraktan Sadarwa na fadar, Steven Cheung, ya kare matakan tsaron da aka dauka. “Akwai makiya da dama na Amurka da ke sanya shugaban a cikin jerin wadanda suke hari, kuma muna amfani da dukkan hanyoyin da muke da su wajen magance wadannan barazanar,” in ji Cheung.
Wannan rahoto ya sake jawo hankali kan irin matakan tsaro na musamman da ake amfani da su wajen kare Shugaba Trump, musamman ganin yadda ake ci gaba da samun barazanar kai masa hari.
Rahotannin sun ce irin wannan dabarar ta tsaro ta taba faruwa a baya. A shekarar 2000, lokacin da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton ya yi amfani da wani jirgin gwamnati da ba a san shi ba wajen shiga Pakistan, yayin da aka yi amfani da Air Force One wajen dauke hankalin jama’a
