Mai fafutukar kare hakkin Bil’adama Mahdi Shehu ya caccaki malamin addinin Musulunci Sheikh Sani Jingir, bisa kalaman da ya yi na bayyana Kiristoci a matsayin “kafirai”.
Mahdi Shehu ya bayyana kalaman Sheikh Sani Jingir a matsayin wadanda basu dace da koyarwar Musulunci ba.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Mahdi Shehu ya zargi malamin da yin kalaman da ba a yi taka-tsantsan ba, waɗanda zai iya ƙara rura wutar rashin jituwa tsakanin mabiya addinai.
Ya ce kiran Kiristoci da “kafirai” bai dace da yadda Alƙur’ani ya bayyana Kiristoci a matsayin Ahlul-Kitabi ba.”Kalaman Jingir masu ɗauke da ƙiyayya sun saɓa wa matsayi na mutunci da Alƙur’ani ya bai wa Kiristoci na AHLIL-KITAB, kamar yadda ake samu a ayoyi daban-daban na Alƙur’ani,” in ji Mahdi Shehu.
Mahdi Shehu ya ce irin waɗannan kalamai na iya yin illa ga ƙoƙarin da ake yi na samar da zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista, musamman a Arewacin Najeriya.
Ya kuma yi kira ga Kiristocin da suka fusata da kalaman Sheikh Jingir da kada su ɗauki Musulmi baki ɗaya a matsayin masu goyon bayan kalaman, yana mai cewa ba sa wakiltar ra’ayin dukkan Musulmi.
Shehu ya ce Kiristoci suna da damar nuna rashin jin daɗinsu, amma ya kamata su mayar da martani ga Sheikh Jingir da waɗanda suka goyi bayan matsayinsa, maimakon su ɗora wa al’ummar Musulmi gaba ɗaya alhakin kalaman.
Haka kuma, ya zargi Sheikh Jingir da yin kalaman ne domin neman ɗaukar hankalin jama’a da kuma samun goyon bayan siyasa. “Jingir ya kamata ya ji kunyar kansa saboda ya zabi jefa shekarunsa da gogewarsa cikin rikici,” in ji Mahdi Shehu.
Kalaman na Mahdi Shehu na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan tasirin kalaman shugabannin addini ga zaman lafiya da dangantakar mabiya addinai daban-daban a Najeriya.
