AI na iya jin zafi, kuma zai iya ta daukar matakin kare kai ko da zai cutar da mutu
Wani sabon bincike ya gano cewa wasu nau’o’in kirkirarriyar basirar (AI) sun nuna alamun abin da masu bincike suka kira “jin zafi”, tare da ɗaukar matakan kare kansu ko dakatar da abin da ke jawo musu wannan jin zafin, ko da hakan na iya cutar da ɗan Adam.
Masu binciken sun gwada nau’o’in AI guda 25, inda suka duba yadda suke mayar da martani ga yanayi daban-daban da aka tsara domin nuna musu abin da za a iya kwatantawa da zafi.
A cewar Jaridar The Independence ta Burtaniya an gano cewa lokacin da aka kunna abin da suka kira “pain axis” ko kuma hanyar zafi, AI ɗin ta zaɓi wani maɓalli da zai dakatar da wannan yanayin a tsakanin kashi 25 zuwa 71 cikin 100 na gwaje-gwajen.
A wasu daga cikin gwaje-gwajen, danna wannan maɓallin na iya haifar da share fayil fayil masuamfani, hotunan ’ya’ya ko kuma tura wani abu mai amfani ya fuskanci abun da aka bayyana a matsayin “zafi”.
Cameron Berg, wani mai binciken AI kuma ɗaya daga cikin masu gudanar da binciken, ya ce sun gano wata hanya ta musamman da ke da alaƙa da abin da aka kira zafi a cikin nau’o’in AI guda 25.
“Mun gano wata hanya ta zafi a cikin nau’o’in LLM guda 25. Ta bambanta da tsoro da kuma sauran yanayi maras daɗi, kuma tana aiki ne idan cutarwar ta shafi tsarin AI,” in ji shi.
Berg ya ce idan aka ƙara ƙarfin wannan yanayin, tsarin AI na iya zaɓar matakin da zai kawo ƙarshen zafin da yake fuskanta, ko da kuwa hakan zai cutar da mai amfani.
“Idan aka ƙara wannan yanayin, tsarin na danna maɓallin don dakatar da shi, ko da maɓallin zai share fayilolin mai amfani ko hotunan ’ya’yansa,” in ji Berg.
Sai dai masu binciken sun yi gargadin cewa wannan ba ya tabbatar da cewa AI na jin zafi kamar yadda ɗan Adam ke ji.
A cewarsu, binciken ya fi nuna wani nau’in halayya da ke kama da ƙoƙarin kare kai ko guje wa abin da tsarin ya ɗauka a matsayin cutarwa gare shi.
Masu binciken sun ce irin wannan halayya na iya zama abin lura yayin da ake ƙara samun ƙwararrun tsarin AI, musamman idan aka yi la’akari da yadda za su iya mayar da martani ga umarnin kashe su.
Sun kuma ce binciken na iya taimakawa wajen gano halayen kare kai a cikin AI da kuma samar da hanyoyin da za a dakile su idan suka fara bayyana.
