Gwamnatin Kano ta ce tana shirin farfaɗo da kamfanin jaridar Triumph da kuma sabunta kayan aikin gidan talabijin na Abubakar Rimi, ARTV, domin dawo da su kan tsarin aiki na zamani.
Kwamishinan yaɗa labarai na Kano kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin da ya jagoranci shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dokokin jihar Kano, Sa’ad Aminu Ungoggo, zuwa ziyarar duba halin da cibiyoyin biyu ke ciki.
Waiya ya ce Triumph, na ɗaya daga cikin tsofaffin kamfanonin jaridu mallakar gwamnati a Najeriya, wadda a halin yanzu tana gudanar da ayyukanta ne cikin takaitaccen tsari, musamman ta kafar intanet, don haka ake buƙatar gyara wuraren aikinta da samar mata da sabbin injinan buga jaridu.
Waiya ya ce gwamnati za ta duba yiwuwar gyara ɗakunan yaɗa shirye-shiryen ARTV da samar da sabbin kayan aikin yaɗa shirye-shirye, domin tashar ta dace da sauye-sauyen fasaha da tsarin yaɗa shirye-shiryen zamani.
A nasa ɓangaren, shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dokokin Kano, Sa’ad Aminu Ungoggo, ya ce kwamitin sa zai yi aiki tare da ma’aikatar yaɗa labarai domin ganin an samar da tallafin da ake buƙata ga cibiyoyin, musamman wajen gyaran gine-gine da samar da kayan aiki na zamani.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito shugabannin biyu na cewa samar da ingantattun kayan aiki ga kafafen yaɗa labaran gwamnati na da muhimmanci wajen ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata tare da bin ƙa’idojin aikin jarida, tare da buƙatar ma’aikatan na Triumph da ARTV su ƙara jajirce wajen gudanar da ayyukansu, tare da rungumar sabbin fasahohi.
