
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kwamishina na daya a hukumar ilimin bai daya ta Jihar Kano (SUBEB), Wada Ibrahim Daho, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda wasu malamai ke shiga ajujuwa ba tare da sun shirya darussa da muhimman takardun koyarwa ba, yana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga ƙoƙarin inganta ilimi a jihar.
Wada Ibrahim Daho, ya bayyana hakan ne yayin da ya jagoranci tawagar manyan jami’an SUBEB zuwa karamar hukumar Rimin Gado domin duba yadda harkokin koyarwa ke gudana a makarantun yankin.
Ya ce manufar tura manyan jami’an hukumar zuwa ƙaramar hukuma guda a lokaci guda ita ce gano matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaban ilimi tare da samar da hanyoyin magance su.

A cewarsa, tawagar ta tantance yadda harkokin koyarwa ke gudana a makarantun yankin, inda ya yaba wa malamai da shugabannin karamar makarantar sakandiren Gulu bisa yadda suke gudanar da ayyukansu.
Sai dai ya nuna damuwa kan yadda wasu malamai a makarantar firamaren Gulu ke yawan makara zuwa aiki duk da kasancewarsu ‘yan asalin garin.
Wada Ibrahim Daho ya umarci sashen ilimi na ƙaramar hukumar da ya ƙara ƙaimi wajen duba makarantu domin tabbatar da cewa malamai suna sauke nauyin da ya rataya a wuyansu yadda ya kamata.
Ya kuma sake jaddada kudurin Hukumar Ilimin bai daya ta Jihar Kano na bijiro da tsare-tsare da manufofi da za su inganta harkokin ilimi a faɗin jihar ta hanyar bibiyar ayyukan malamai da makarantu domin tabbatar da ana gudanar da ayyukan koyarwa yadda ya kamata.
Haka kuma, kwamishinan ya bayyana cewa akwai raunin a shugabanci da gudanarwar wasu makarantu da aka ziyarta.
Ya kuma umarci sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar da ya yi sauye-sauyen wuraren aiki ga wasu shugabannin makarantu domin inganta tsarin shugabanci da gudanarwa a makarantun da abin ya shafa.
A nasa bangaren sakataren Ilimi na yankin Abdullahi Sabiu ya ce sashen ilimi na ƙaramar hukumar zai gudanar da zama na musamman domin nazari da bibiyar dukkan matsalolin da aka gano tare da aiwatar da shawarwari da umarnin da aka ba su, domin tabbatar da samun ci gaba mai ɗorewa a fannin ilimi.
