Gwamnatin Kano ta ce zata rabawa manoman jihar tallafin takin zamani tirela 150 da kuma yin ragin kaso 50 cikin 100 kan wanda zata siyar musu, da nufin bunkasa tattalin arzikin su da wadata Kano da abinci.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ambata hakan, yayin da yake mikawa sabon dan majalisar tarayya mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa shaidar da ta cin zabe.
Gwamna Yusuf ya ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatin sa na tallafawa manoma, karfafa samar da abinci da kuma habaka tattalin arzikin al’ummar Kano.
Gwamnan ya kuma gargadi shugabann kananan hukumomin Kano da sauran masu ruwa da tsaki cewar, bai amince idan anbasu takin su raba shi a sakatariyar kowace karamar hukuma ba, sai dai su nemi gidan mai sarautar gargajiya a yankin da suke domin ya kai ga ƙananun manoma da gujewa kitso da kwarkwata.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa gwamnatin jihar ta ce za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar manoma tare da tabbatar da wadatar abinci a Kano da ma kasa baki daya.
