
Jam’iyyar PDP ta baiwa tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, takardar tabbatar da tsayawa takarar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen shekarar 2027.
An ba shi takardar ne a ranar Laraba yayin taron Kwamitin Zartarwar jam’iyyar na Ƙasa (NEC) da kuma rantsar da sabbin mambobin kwamitin na wa’adin 2026 zuwa 2030.
Shugaban PDP na ƙasa, Abdulrahman Mohammed ne, ya jagoranci taron wanda aka gudanar a shelkwatar jam’iyyar dake Abuja.
Jam’iyyar ta ce shugabancin Abdulrahman ya samu amincewar Kotun Ƙoli da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
A yayin taron, jam’iyyar ta bai wa ’yan takarar gwamna daga jihohi daban-daban takardun tabbatar da tsayawa takara bayan amincewa da sunayensu a hukumance.
Wannan na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shirye tunkarar babban zaɓen 2027
