
Hukumar kula da sanya hannun jari ta kasa ta haramtawa matatar mai ta Ɗangote sayar da hannayen jari, sakamakon gaza cika wasu ƙa’idoji da suka haɗar da rashin samun sahalewa daga hukumar.
Wannan umarni na cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar bayan tallan fara sayar da hannayen jari da matatar ta fitar, da ke neman al’umma su sayi hannun jari.
Hukumar ta cikin sanarwar ta ce doka ta fayyace cewa ya zama wajibi kamfani yayi rajista da ita, tare da cika wasu ka’idoji kafin fara sayar da hannayen jari kuma wannan matata bata cika su ba.
Baya ga haka kuma hukumar ta haramtawa matatar ta Ɗangote ci gaba da saka talluka da ke bayyanawa jama’a muhimmncin siyan hannun jari har sai an warware matsalar da ke tsakaninsu.
Haka kuma hukumar ta shawarci jama’a da su kaucewa sanya hannun jari a matatar ta Ɗangote a halin yanzu don kaucewa tafka asara.
