Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta ce ta gurfanar da direbobi 123 a gaban kotu bayan kama su da laifin amfani da motocin da ba su da lambar rajista ko kuma masu amfani da lambobin da aka rufe, a ƙarƙashin aikin “Operation Clean Plates.”
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Litinin a hedikwatar rundunar da ke Bompai.
A cewarsa, tun bayan ƙaddamar da aikin a ranar 6 ga Yuli, jami’an rundunar sun kama motoci 123 da suka saɓa wa dokokin zirga-zirga a ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano, inda aka gurfanar da direbobinsu domin fuskantar hukunci bisa tanadin doka.
Bakori ya ce manufar Operation Clean Plates ita ce dakile amfani da motocin da ba su da cikakkiyar shaidar rajista, yana mai bayyana cewa masu aikata laifuka kan yi amfani da irin waɗannan motoci wajen ɓoye asalinsu da kuma kauce wa kama su.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aiwatar da aikin domin tabbatar da tsaro, bin doka da oda, tare da rage ayyukan masu laifi a faɗin Jihar Kano.
