Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da sabon tsarin mayar da tubabbun yan ta’adda cikin al’umma da rikice-rikice suka shafa.
Jami’in kula da Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC) a Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Adamu Laka, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin taron tantance ƙa’idojin aiwatar da shirin Kwance Ɗamara, Rushe Runduna da Sake Haɗa Mutane da Al’umma (DDR) a Abuja.
Ya ce sabon tsarin na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin magance matsalar tsaro ta hanyar da ba ta dogara da ƙarfin soja kaɗai ba, tare da samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankunan da rikice-rikice suka shafa.
Laka ya bayyana cewa ƙa’idojin za su taimaka wajen tabbatar da haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da farar hula, tare da fayyace ayyukan kowacce hukuma da kuma ƙarfafa gaskiya da riƙon amana wajen aiwatar da shirin.
A cewarsa, an tsara sabon shirin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, tare da la’akari da ƙwarewar Najeriya da kuma dabarun da sauran ƙasashe ke amfani da su wajen sake haɗa tsofaffin mayaƙa cikin al’umma.
Za a fara aiwatar da shirin a jihohin Kaduna, Katsina da Zamfara, kafin a faɗaɗa shi zuwa sauran sassan ƙasar nan.
