Gwamnatin Kano ta ce ta fara aiwatar da manyan sauye-sauyen da za su ƙarfafa ayyukan hukumar kare haƙƙin masu saye da siyarwa ta jihar, da nufin dakile yaɗuwar jabun kayayyaki da hana siyar da waɗanda wa’adin amfaninsu ya ƙare a faɗin jihar.
Shugaban hukumar kare hakkin mai saye da sayarwa ta jihar Dr Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana hakan yayin da yake zayyana wasu daga nasarorin da hukumar ta samu tun bayan da ya karɓi ragamar jagorancin ta.
Dr Garba ya ce tuni hukumar ta sake fasalin tsarin gudanar da ayyukan ta, wanda hakan ya sanya kawo yanzu ta karɓi koke-koke sama da 200 daga sassa daban-daban na Kano, tare da ƙarawa ma’aikatan ta horo domin inganta ƙwarewa da nagartar su a bakin aiki.
Dr Garba ya ce hukumar ta sake ƙarfafa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin yaƙi da jabun kayayyaki, tare da ƙaddamar da shafinta na yanar gizo da lambobin waya na karɓar koke-koken jama’a domin sauƙaƙa kai mata rahoton matsaloli da ɗaukar matakin gaggawa.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Shugaban Hukumar na yin kira ga al’ummar Kano da su riƙa kai rahoton duk wani kaya na jabu, wanda ya lalace ko kuma ba shi da inganci, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya da adalci domin kare lafiyar jama’ar Kano.
